24 Yuni 2021 - 13:02
Taron Tunawa Da Zagayowar Lokacin Haihuwar Imam Ridha (AS) Jikan Manzon Allah (SAW) A Kenya

an gudanar da taron tunawa da zagayowar lokacin haihuwar Imam Ridha (AS) a Kenya.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, an gudanar da taron murnar zagayowar lokacin haihuwar Imam Ridha (AS) jikan manzon Allah (SAW) a birnin Nairobi na kasar Kenya a daren jiya Litinin.

Taron ya samu halartar malamai da kuma wasu daga cikin masana gami da daliban wasu cibiyoyin ilimin addini, da kuma wasu baki 'yan kasashen ketare da suke zaunea  birnin Nairobi.

An gabatar da jawabai dangane ad madaukakin matsayi na Imam ridha (AS) da kuma iyalan gidan manzon Allah (SAW).

Imam Ridha (AS) shi ne Imami na takwas daga limaman ahlul bait (AS) wadanda suke jagorancin al'ummar kakansu (SAW).

342/